A Alhamis din nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa kasar Sin ta shirya tsaf domin gudanar da taron dandalin tattaunawar koli ta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa game da shawarar "ziri daya hanya daya".
Mista Geng ya fadi hakan ne, a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya kara da cewa, kasar Sin tana fatan amfani da wannan dama, wajen tattaunawa da abokanta game da manyan manufofi, da kafa dandalin da zai bude kofa ga kowa da kowa, da cin gajiyar bunkasuwa tare.
Ya zuwa yanzu, shugabanni 29 na kasashen duniya, da shugabanni 3 na muhimman kungiyoyin kasa da kasa kamar MDD, za su halarci taron shugabanni da sauran harkoki. (Tasallah Yuan)