Wang Xiaotao ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, za a gudanar da taron kolin ne a ranar 14 ga wata, inda za a tattauna ababen more rayuwa, da zuba jari, da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da makamashi, da hada-hadar kudi, da musayar al'adu, da yanayin halittu, da kuma hadin gwiwa a kan teku, don a gano hanyar da za a dosa.
Haka zalika, Wang Xiaotao ya ce, za a gudanar da cikakken zama daya da taruruka shida yayin da ake gudanar da taron kolin. Tarurukan shida za su maida hankali ga tuntubar juna kan manufofi, hadin gwiwar raya ayyukan more rayuwa, sa kaimi ga yin cinikayya cikin sauki, da hada-hadar kudi, da mu'amalar jama'a da kuma musayar ra'ayoyi a tsakanin masana. (Zainab)