in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya kalubalanci bangarori daban daban na Guinea Bissau da su warware rikicin siyasar dake tsakaninsu
2017-05-12 11:16:17 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayar da sanarwa a jiya Alhamis, inda ya nuna damuwa game da rikicin siyasar da kasar Guinea Bissau ke fuskanta, ya kuma kalubalanci bangarori daban daban na kasar da su magance tsanantar rikicin, su kuma warware shi ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar siyasa da aka cimma a da.

Sanarwar ta bayyana cewa, kwamitin sulhun MDD ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Guinea Bissau da su maida hankali ga muradun jama'a, da maido da zaman lafiya a fannin siyasar kasar, tare da warware rikicin siyasa cikin hanzari. Kana ya nuna damuwa ga batutuwan da suka shafi aikata manyan laifufuka a tsakanin kasashen duniya da masu tsattsauran ra'ayi, barazanar ta'addancin da kasar ke fuskanta.

A watan Agustan shekarar 2015 ne, aka samu rashin jituwa tsakanin bangarori daban daban na kasar Guinea Bissau dangane da batun nada firaministan kasar, lamarin da ya haifar da rikicin siyasa a kasar. A watan Nuwanban shekarar 2016, shugaban kasar José Mário Vaz ya nada mai ba da shawara ga tsohon shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo a matsayin firaministan kasar, amma kungiyar 'yan adawa ta ki amincewa da nadin nasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China