in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Guinee-Bissau za su ci gaba da karfafa dangantakar kud da kud
2016-08-02 09:38:49 cri
Jakadan kasar Sin dake kasar Guinee-Bissau, Wang Hua, ya bayyana a ranar Litinin cewa Beijing da Bissau za su kara karfafa huldar dangantakarsu, musamman ma a fannonin noma, ilimi da kamun kifi.

Jakadan Sin din ya yi wannan furuci ne bayan wata ganawa tare da sakataren kasa dake kula dangantaka, Augusto Poquena.

Bangarorin biyu sun bayyana burinsu na moriyar juna wajen yin aiki tare domin tabbatar da wani ci gaba mafi albarka ga al'ummomin kasashen biyu, in ji mista Wang.

A cewar jakadan Sin, kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa Guinee-Bissau.

Kasar Sin, na daya daga cikin muhimman kasashen abokan huldar ci gaba na kasar Guinee-Bissau, kuma mai taimakawa bangarorin noma da ababen more rayuwa sosai, in ji mista Wang.

Baya bayan nan, gwamnatin Sin ta baiwa Guinee-Bissau kayayyaki na darajar dalar Amurka miliyan 1,25 domin taimaka kasar kara bunkasa nomanta na shinkafa.

A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan aiki da gine gine, Malam Banjai, ya tabbatar da cewa Sin babbar abokiyar huldar dangantaka ce ta kasar Guinee-Bissau, don haka akwai bukatar a mai da hankali na musamman. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China