in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu raguwar cutar sankarau da ta bulla a Najeriya
2017-05-12 10:12:15 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, an samu lafawar cutar sankarau da ta barke a galibin jihihon kasar.

Wata sanarwa da kakakin cibiyar kare yaduwar cututtuka ta kasar(NCDC) Lawal Bakare ya rabawa manema labarai ta bayyana cewa, tuni cibiyar ta dauki matakan da suka dace don hana barkewar cutar a nan gaba, ta kuma shirya tsaf don kara samar da magungunan cutar.

Bakare ya ce, gangamin wayar da kan jama'a na farko da hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa ta gudanar a jihar Zamfana da kuma wanda ya gudana daga bisani a jihar Sokoto game da alluran riga kafin cutar sun yi nasara, duba da yadda jama'a ke yin tururuwa zuwa cibiyoyin alluran riga kafin da aka bude. Ya ce gwamnatocin jihohin kasar a nasu bangare su ma suna shirya gangamin wayar da kan jama'a, don tabbatar da cewa, shirin alluran riga-kafin cutar ya kai ga al'ummomin dake cikin hadari kamuwa da cutar.

Jami'in cibiyar ya ce gwamnati da abokan hulda za su ci gaba da yin aiki kafada da kafada don ganin an rage kuncin da cutar da haifar kan wasu al'ummomi tare da tabbatar da cewa, an dakile barkewar cutar baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China