Kwamishinan Lafiya na jihar Kabiru Ibrahim Getso, ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, gwamnati ta inganta matakan sa ido a wasu kananan hukumomin jihar.
Ya kara da cewa, gwamnatin ta kuma dauki matakan da suka dace na takaita yaduwar cutukan, inda ya ce, an samu rahoton mutane 20 da suka kamu da cutar sankarau a kananan hukumomin jihar 8, inda daga cikinsu, mutane hudu ne kawai aka tabbatar da sun kamu da cutar.
Kabiru Getso ya ce ayarin masu kai daukin gaggawa na jihar ya sake fara aikin, yana mai cewa an kuma samar musu da magunguna.
Har ila yau ya ce gwamnati ta ba dukkan al'ummar jihar umarnin kara kula da yin taka-tsantsan, tare da gaggauta zuwa asibiti mafi kusa idan suka ji alamomin matsanancin ciwo kai ko zazzabi ko amai ko kuma rikewar wuya.
Bugu da kari, Kwamishinan lafiyar ya ce an bude layukan sadarwa domin taimakwa wajen takaita yaduwar cutukan, inda kuma ake wayar da kan mutane game da alamominsu ta kafafen yada labarai. (Fa'iza Mustapha)