An yi mace-macen ne cikin watanni shida da suka gabata a kusan jihohi 15, ciki har da jihohi 5 na arewacin kasar da birnin tarayya Abuja.
Shugabar sashen sanya ido kan cutuka na cibiyar Olubunmi Ojo, ta ce cutar ta fi kamari a Birnin Abuja da jihohi 5 na arewacin kasar da suka hada da Katsina da Kebbi da Niger da Sokoto da kuma zamfara.
Ministan Lafiya na Kasar Isaac Adewole, ya ce an shigar da sabuwar kwayar cuta da ba a saba gani ba a Nijeriya daga makwaciyarta Jamhuriyar Nijar, ya na mai cewa cutar na bukatar nau'o'i daban-daban na rigakafi.
Zuwa ranar Litinin da ta gabata, jimilar mutane 1, 828 ne suka kamu da cutar a kasar dake yammacin Afrika.
A wani bangare na yaki da cutar, Gwamnatin Nijerya ta tura masana kan binciken musababbin barkewar cutuka a cikin al'umma da allurar rigakafi zuwa yankunan da abun ya shafa.
Haka zalika, gwamnatin ta ce tana aiki tare da hadin giwar hukumomin agaji na duniya, ciki har da hukumar lafiya ta duniya WHO domin shawo kan cutar. (Fa'iza Mustapha)