Abdullahi Gada, wani kwararren likita ne a yankin, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an samu rahoton bullar cutar sau 77 a karamar hukumar Gada dake arewacin Najeriya.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin Najeriya, ta sanar da tura tawagar kwararrun masana cututtuka masu saurin yaduwa da kuma alluran rigakafi zuwa yankin domin dakile annobar da ta yadu har zuwa jahar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.
Ministan lafiya na Najeriya Isaac Adewole ya bayyna cewa sabbin kwayoyin cutar da suka bazu a Najeriya, an shigar dasu kasar ne daga makwabciyarta jamhuriyar Nijer, ya kara da cewa cutar tana bukatar nau'in rigakafi na daban.
Idan za'a iya tunawa mutane sama da 156 ne suka mutu a Najeriyar a shekarar 2009, a lokacin da irin wannan cutar da bulla a kasar.
Da yake karin haske game da barkewar cutar, Gada yace an yi nasarar shawo kan cutar a halin yanzu. Kuma mutane 10 ne aka kwantar a asibiti domin yi musu magani.