in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya: fashewar nakiya ta kashe sojoji 9
2017-04-24 10:33:15 cri
'Yan sandan kasar Somaliya sun tabbatar da cewa, a jiya Lahadi an samu fashewar wata nakiya da aka binne a karkashin kasa, a yankin Puntland dake arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 9, tare da raunatar wasu 3.

A cewar 'yan sandan kasar, fashewar ta abku ne a garin Glgala dake yankin Puntland. Kuma ga alama an tsara lamarin ne musamman domin hallaka sojojin gwamnatin dake wurin, wadanda ke kokarin dakile masu tsattsauran ra'ayi na kungiyar Al-Shabab.

A nata bangare, kungiyar Al-Shabab ta dau alhakin kai wannan hari, bayan abkuwar sa.

Don kau da kungiyar Al-Shabab, wadda ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Al-Qaida, sojojin gwamnatin kasar Somaliya, da hadin gwiwar sojojin kungiyar tarayyar Afirka AU, sun gudanar da jerin matakan soja a kasar Somaliya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China