in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana kokarin karfafa shirin yaki da cin hanci da rashawa
2017-04-27 20:13:07 cri
Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa Ibrahim Magu, ya bayyana cewa, Najeriya tana kokarin ganin ta karfafa shirinta na yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar sanya ido kan kowane bangare na tattalin arzikin kasar.

Magu wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Abuja,fadar mulkin kasar, ya kuma bayyana cewa, shirin zai kuma magance matsalolin rashin biyan haraji a sassa daban-daban na kasar, ganin yadda hukumar ta EFFCC ta fara hukunta masu kin biyan haraji a kasar.

Ya kuma bayyana cewa, za a fadada shirin yaki da cin hancin zuwa jami'o'in kasar, ta hanyar ilimantar da dalibai game da bukatar kaucewa karbar cin hanci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China