in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren kunar bakin wake sun halaka mutane biyar a arewa maso gabashin Najeriya
2017-04-26 20:37:56 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu 'yan kunar bakin wajen sun tayar da wasu abubuwan fashewa a wurare daban-daban guda uku a yankin Muna na jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar dake fama da tashin hankali.

Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar(NEMA) mai kula da yankin Abdulkadir Ibrahim ya bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa, mutane biyar ne suka gamu da ajalinsu kana wasu 11 suka jikkata sanadiyar lamarin da ya faru da misalin karfe 4 da minti 11 na safe agogon wurin.

Jami'in ya ce, 'yan kunar bakin wake guda hudu da kuma dan kato da goro na daga cikin wadanda suka mutu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China