Babban mataimaki na musammam ga shugaban kasar kan masu bukata ta musammam Samuel Ankeli ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar.
Samuel Ankeli, ya ce Gwamnati na kokari samar da manufofi da za su kunshi masu bukata ta musammam, a kokarin tabbatar da cimma muradun ci gaba masu dorewa.
A cewarsa, Gwamnati mai ci na son gyara kurakuran da aka tafka a baya, inda aka bar masu bukata ta musammam a baya, ta fuskar rashin tallafa musu da samar musu da ayyukan yi.
Ya shaidawa manema labarai cewa, baya ga kiwon lafiya da ilimi da samar musu da matsuguni da tallafi, samar da ayyukan yi na daga cikin muhimman bangarori da suka dame Gwamnati da masu bukata ta musammam.
Ya ce gwamnati ta samar da muhimman manufofi, yana mai cewa aikin ofishinsa shi ne, sa ido da kuma tabbatar da aiwatar da manufofin yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)