Lavrov ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi a birnin Moscow, inda ya ce, NATO ta taba yunkurin sarrafa kasar Ukraine, da kuma shigar da kasar a kungiyar. A sa'i daya kuma ta yi shirin kewayen kasar Rasha a fannin soja ta hanyar amfani da batun kasar Crimea, amma dukkan shirye-shiryenta sun ci tura.
Lavrov ya kara da cewa, sakamakon fushi da kunya ne kungiyar NATO ta dakatar da duk irin hadin kai a tsakaninta da Rasha, ciki har da fannin yaki da ta'addanci.
A cewarsa, yanzu kungiyar NATO na fatan farfado da shawarwari tare da Rasha, kasar Rasha ma a shirye take a kai. Amma, duk da haka sai dai bisa tushen zaman daidai wa daida da nuna girmamawa ga juna ne kasar Rasha za ta yi shawarwari tare da kungiyar ta NATO. (Bilkisu)