in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta yi kira da kafa kawancen yaki da ta'addanci a duniya
2017-04-06 13:29:58 cri

Kasar Rasha ta tsaurara matakan tsaro da yaki da ta'addanci, sakamakon harin da aka kai cikin wani jirgin kasan karkashin kasa a birnin St. Petersburg na kasar.

A jiya ne kuma, madam Maria Zakharova, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, ta ce bai kamata a nuna fuska biyu wajen yaki da 'yan ta'adda ba, tana mai cewa, kamata ya yi kasahen duniya su amsa kiran Rasha na kulla kawance ta fuskar yaki da ta'addanci.

Kafin wannan kuma, shugaba Vladimir Putin na kasar ya sha yin kira da a inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya ta fuskar yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China