in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha tace sabon takunkumin da Amurka ta saka mata ya ci karo da manufofinta na yaki da ta'addanci
2017-03-27 10:40:55 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha tace sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa kamfanonin kasar Rashar ya ci karo da alkawurran da Amurkar ta yi na bada fifiko wajen yaki da ayyukan ta'addanci.

Jami'an ma'aikatar tsaron Amurka sun sanar cewar an zartar da hukunci kan wasu kamfanonin kasar Rasha 8 saboda saba dokoki game da batun kasashen Iran, da Korea ta arewa, da kuma dokar hana yaduwar makamai ta Syria wato (INKSNA).

Dokar ta INKSNA ta amincewa Amurka ta aza takunkumi kan duk wani mutum, ko kungiya ko kuma gwamnatoci na kasashen waje da aka samu da hannu wajen bada damar yaduwar makamai a tsakanin alumma.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rashar Maria Zakharova, tace matakin da Amurka ta dauka na hukunta kamfanonin na Rasha, ya hada da masu kera kananan jirage da horas da kwararrun matukan jiragen, ya kasance abin takaici kuma mai cike da rudani.

Sai dai a cewarta mahukunta Amurkar basu ce uffan ba game da dalilan da suka sa su daukar wannan mataki, amma suna danganta batun ne da dokokin da suka haramtawa duk wani mutum ko kungiya da ta hada kai da Iran da kumaSyria.

Zakharova tace, wannan takunkumi ba zai iya haifar da wata babbar illa ba ga Rashar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China