in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 9 'yan kasar Chadi
2017-05-06 11:32:06 cri

Rundunar sojin Chadi, ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojinta 9, a wani hari da suka kai musu yayin da suke bakin aiki a yankin tafkin chadi.

Kakakin rundunar sojin Azem Bagouna, wanda ya ce su ma sojojin sun kashe kimanin mahara 40, ya ce an kai harin ne da sanyin safiyar jiya Jumma'a da misalin karfe 4 agogon GMT, lokacin da sojojin ke bakin aikinsu a garin Kaiga-Kindiria dake iyakar Nijeriya da Chadi.

Ya kuma kara da cewa, sojojin na Chadi sun mai da martini ga maharan.

Ko a ranar 1 ga watan Nuwamban shekarar 2015, wasu hare-hare biyu da Boko Haram ta kai, sun yi sanadin mutuwar sojojin Chadi 3 tare da jikkata wasu 14 a yankunan Bohama da Kaiga-Kindiria, inda su kuma sojojin suka hallaka mayakan kungiyar 16. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China