Wasu mata 'yan kunar bakin wake su 3 sun rasa rayukan su, yayin da suke yunkurin kaddamar da hari a kauyen Mamanti dake kusa da birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno a tarayyar Najeriya.
Lamarin ya faru ne a jiya Litinin, kamar dai yadda jami'an tsaron yankin suka tabbatar. An ce an harbe biyu daga cikin su ne har lahira, bayan da aka gano take-taken su na kaddamar da hari kuma suka yi kokarin tserewa, yayin da dayar kuma bam din da ke jikin ta ya tashi, nan take kuma yi sanadiyyar mutuwar ta.
Da yake tabbatar da aukuwar lamari, kwamishinan 'yan sandan jihar ta Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Damian Chukwu, ya ce akwai kyakkyawan zaton cewa matan, magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram ne, kungiyar da ya zuwa yanzu ta hallaka mutane da yawan su ya haura 20,000, tare da raba wasu kusan miliyan 2.3 da gidajen su, tun fara kaddamar da hare haren ta a shekarar 2009.
Tuni dai rundunar 'yan sanda ta aike da jami'an ta na sashen kwance ababen fashewa zuwa wurin da lamarin ya auku, da nufin tabbatar da tsaro. Yayin da dakarun tsaron gwamnati ke kara kaimin sintiri ta sama da kasa, a daukacin sassan yankin arewa maso gabashin kasar.(Saminu)