Mr. Geng wanda ya amsa a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana, akwai tambaya cewa, mene ne ra'ayin Sin game da bayanin da kamfanin dillancin labaru na Koriya ta Arewa ya bayar inda ya zargi Sin da ta yi matsin lamba ga sakawa kasar Koriya ta Arewa takunkumi?
Geng Shuang ya bayyana cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da tabbatar da zaman lafiya da na karko a zirin, da sa kaimi ga warware batun ta hanyar yin shawarwari. Sin tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su dauki alhakinsu da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da rayuwar jama'a a yankin. (Zainab)