in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci a nuna sanin ya-kamata a fannin daidaita batun nukiliya a zirin Koriya
2017-04-24 10:18:44 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya jaddada bukatar nuna sanin ya-kamata, da tsayawa kan yunkurin neman sulhu, yayin da ake kokarin daidaita al'amura a zirin Koriya, maimakon nuna kiyayya ga juna, wanda aka dade ana yi a kwanakin baya.

Ministan na kasar Sin ya yi furucin ne a wajen wani taron manema labaru da ya gudana a kasar Girka a jiya Lahadi, wanda shi da takwaransa na kasar Girka suka halarta tare.

A cewar ministan, kasar Sin ta riga ta bayyana ra'ayinta dangane da batun zirin Koriya sarai, wanda kuma ba za ta canza ba, wato tana goyon bayan akidar nacewa kan yunkurin kau da makaman nukiliya daga zirin, da nacewa ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Don neman cimma wannan buri, a cewar mista Wang Yi, dole ne a bi hanyar sulhu wajen daidaita batun nukiliya a zirin Koriya. Wang ya kara da cewa, kasar Sin tana kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, wajen daidaita al'amura a zirin na Koriya, tare da neman sake bude shawarwarin sulhu. Sa'an nan a kwanakin baya, kasar ta sake gabatar da wasu shawarwari masu kyau, wadanda suka samu goyon baya daga sauran kasashe da yawa. Bisa yanayin da ake ciki na fama da matsala, a kokarin sulhuntawa tsakanin bangarori masu alaka da batun zirin Koriya, kasar Sin za ta ci gaba da musayar ra'ayi da su, tare da samar da gudunmawa, a yunkurin daidaita batun nukiliya a zirin Koriya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China