in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CCDI na matsa kaimi wajen yaki da cin hanci a kasar Sin
2017-01-09 10:11:18 cri

Hukumar sanya ido da yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa ta kasar Sin ko CCDI, ta sake jaddada aniyar ta, ta matsa kaimi wajen dakile laifuka masu nasaba da aikata zamba ko almundahana a daukacin fadin kasar cikin wannan sabuwar shekara ta 2017.

Wata sanarwar bayan taro da aka fitar, bayan kammala zama na 7 na kwamitin tsakiya karo 18 na JKS, wanda ya gudana a tsakanin ranekun Juma'a da Lahadi, ta bayyana cewa, akwai bukatar hadin gwiwa a fannin sa ido kan harkokin jam'iyya, da tabbatar da bin ka'ida wajen zabe da karin girma tsakanin 'ya'yan jam'iyya, domin tabbatar da zabar jami'ai na gari, a matakan jagoranci na koli da na kananan hukumomi.

Shugaban kasar Sin kuma babban sakatare janar na JKS Xi Jinping, na cikin manyan jagorori da suka halarci wannan taro. Kaza lika taron ya samu halartar firaministan kasar Li Keqiang, da sauran shugabannin Zhang Dejiang, da Yu Zhengsheng, da Liu Yunshan, da Wang Qishan da kuma Zhang Gaoli.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China