Al'amarin ya auku ne a wani gidan kallo a Calabar babban birnin jihar Cross River a ranar Alhamis, da misalin karfe 9:30 na dare agogon Nijeriya, a lokacin da ake qasar kwallon kafa na nahiyar Turai tsakanin kungiyoyin Manchester United da kuma Anderlecht.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Hafiz Inuwa ne ya tabbatar da aukuwar hatsarin, yayin wani taron manema labarai da ya kira jiya Jumma'a a Calabar.
Hafiz Inuwa, ya ce kiran taron manema labaran ya zama wajibi, la'akari da yadda wasu jaridun kasar da masu rubutu a shafin intanet ke cewa mutane sama da 30 ne suka rasa rayukansu yayin hatsarin.
Ya ce a hakikanin gaskiya, mutane 18 ne al'amarin ya rutsa da su, kuma an garzaya da su asibitin koyarwa na Jami'ar Calabar.
A nata bangare, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayyana alhinin mutuwar magoya bayan kwallon kafar na birnin Calabar. (Fa'iza Mustapha)