Kakakin rundunar 'yan sandan Jimoh Mashod, ya shaidawa manema labarai ranar Juma'a a Abuja babban birnin kasar cewa, ana neman Akwaza wanda aka fi sani da 'Ghana' saboda alakar da yake da ita da kisan mutane 17 a ranar 20 ga watan Maris din da ya gabata a garin Zaki Biam na jihar Benue.
Jimoh Mashod ya kuma yi holin wasu mutane 19 da ake zargin na da alaka da kisan, ciki har da mata biyu.
Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, wanda ake neman shi ne jagoran kungiyar da ta yi kaurin suna wajen kisan dauke dai-dai, dake da alhakin kisan wasu mutane 50 a yankuna daban-daban na jihar ta Benue.
Haka zalika, ana zargin Akwaza da laifuka da suka hada da sace mutane domin karbar kudin fansa da fashi da makami da tada rikicin kungiyar asiri da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan jihar.
Har ila yau, Mashod ya ce bincike ya bayyana cewa, Akwaza ne ke da alhakin kashe Desen Igbana, mashawarci na musammam ga Gwamnan Jihar Samuel Ortom kan harkokin tsaro.
Ya kuma ce mutanen da aka yi holin na su, na hannun rundunar 'yan sanda, kuma nan bada dadewa ba, za a shigar da kararsu a gaban kuliya. (Fa'iza Mustapha)