Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama na kasar ya tabbatar da cewa aikin gyare gyaren da aka gudanar na tsawon makonni 6 ya kammala tsab, kuma aikin ya cika ka'idojin hukumar lura da sufurin jiragen sama ta kasa da kasa (ICAO) kuma sun gamsu da aiki.
Jami'in yace a halin yanzu jiragen saman zasu iya cigaba da sauka ko tashi daga filin jirgin saman.
A ranar 8 ga watan Maris ne gwamnatin Najeriya ta bada sanarwar rufe filin jiragen saman na Abuja na wucin gadi, domin gudanar da gyaran titunan filin jirgin, wanda ya kamata a gyara su bayan yin amfani dasu na tsawon shekaru 20, amma an shafe sama da shekaru 34 ana amfani da su ba tare da gudanar da gyaran ba.