A cikin wasikar, shugaba Xi ya jaddada cewa, wannan tsarin ya kasance tsarin musayar al'adu mai muhimmanci matuka na farko da kasar Sin ta bullo da shi tare da kasashen Afrika, kana muhimmin mataki wajen tabbatar da nasarorin da aka samu a taron kolin Johnnesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Gudanar da tsarin zai inganta harsashin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a fannin ra'ayin jama'a, tare kuma da inganta musayar al'adu a tsakaninsu.
Baya ga haka shugaba Xi ya nuna cewa, a yayin bukukuwan da za a shirya a gun taron, za a kira taron ministoci na hadin kan aikin kiwon lafiya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Wannan hadin kai wani muhimmin sashe ne na hadin kan abokantaka tsakanin bangarorin biyu. Shugaba Xi yana mai fatan za a hada kai tsakanin bangarori daban daban da batun ya shafa, don zurfafa hadin kan aikin jinya tsakanin Sin da kasashen Afirka, da nufin samar da alheri ga jama'arsu.
A nasa bangaren, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma shi ma ya aike sakon fatan alheri ga taron, inda ya bayyana cewa, kafuwar tsarin musayar al'adun bisa babban matsayi a tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu ya kara shaida kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya yi imanin cewa, tsarin zai inganta hadin kai da cudanya da juna a fannonin da batun ya shafa, da karfafa fahimtar juna a tsakanin jama'ar kasashen biyu, ta yadda za a daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, kana da tabbatar da samun wadata tare. (Bilkisu)