Kakakin ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar Sin Wu Chungeng wanda ya bayyana hakan jiya a taron manema labarai ya bayyana cewa, yarjeniyoyin da aka sanyawa hannu sama da shekaru ukun da suka gabata sun hada da sufurin jiragen kasa da na mota da kuma ruwa sai kuma harkokin aikewa da wasiku.
Wu ya ce, bangaren sufuri shi ne ginshikin aiwatar da shirin na Ziri daya da hanya daya.Ya kuma ce kasar Sin ta bude hanyoyin sufuri da na zirga-zirgar jama'a na kasa da kasa 356, baya ga hidimomin sufurin ruwa da za su karade dukkan kasashen da suka ratsa shirin na ziri daya da hanya daya.
Kakakin ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana shirin yin hadin gwiwa a bangaren samar da harkokin sufuri mai inganci, da gina hanyoyin mota da na ruwa tare da inganta yanayin sufurin kasa da kasa.
A sheakar 2013 ne kasar Sin ta bullo da shirin na Ziri da hanya daya,wanda zai hade yankin Asiya da Turai da kuma nahiyar Afirka,da nufin raya kasa tsakanin dukkan wadannan kasashen.(Ibrahim)