Yau Alhamis mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, ya gana da ministan harkokin wajen Eritrea Osman Saleh a nan Beijing.
A yayin ganawar tasu, mista Yang ya yi fatan kasashen 2 za su aiwatar da sakamakon da aka samu, a yayin taron koli na Johannesburg, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, za su kuma kara habaka hadin gwiwar moriyar juna, da sada zumunta a sassa daban daban, a kokarin raya huldar da ke tsakaninsu zuwa sabon mataki.
A nasa bangare, Osman Saleh ya yi fatan kara yin hadin kai da kasar Sin, domin samun moriyar juna, tare da sa ran ganin kasar Sin ta kara taka rawa a al'amuran kasa da kasa da na Afirka. (Tasallah Yuan)