in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da bakin kasasr Eritrea
2017-04-20 20:18:19 cri

Yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Eritrea Osman Saleh, da jagoran ofishin harkokin siyasa na jam'iyyar PFDJ Yemane Gebreab a nan Beijing.

A yayin ganawar tasu, Mr Li Yuanchao, ya yi fatan kasashen 2 za su aiwatar da sakamakon da aka cimma, a yayin taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, da kuma kokarin zurfafa hadin gwiwar sassan yadda ya kamata, ta yadda za a sada jama'ar kasashen biyu da alherai.

A nasa bangaren, Osman Saleh ya yi fatan zurfafa dankon zumunta tsakanin kasar Eritrea da Sin, da kyautata hadin gwiwa tsakaninsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China