in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun AU sun kwace iko da garin Badade na Somalia daga hannun Kungiyar Al-Shabaab
2017-01-25 09:47:06 cri

Shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika AU, dake aiki a Somalia wato AMISOM, ya ce dakarunsa da na gwamnatin Somali sun kwace iko da garin Badade dake yankin kudancin kasar, daga hannun kungiyar Al-Shabaab.

Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya, AMISOM ta ce dakarun na hadin gwiwa, sun kashe tare da jikkata mayakan Al-Shabaab da dama a farmakin da suka kai.

Rahotanni sun ce mayakan sun kaddamar da wani hari a jiya da yamma, a yunkurinsu na sake kwace iko da garin na Badade dake kusa da iyakar kasar da Kenya.

Garin Badade dake da nisan kilomita 200 daga birnin Kismayo, ya fada hannun kungiyar Al-Shabaab ne bayan dakarun kasar Kenya sun janye daga shirin na AMISOM a watan Janairun bara.

Har yanzu, kungiyar Al-Shabaab na rike da wasu yankunan tsakiya da kudancin Somalia.

Kungiyar dai ta shafe shekaru goma tana yaki da gwamnatin kasar, kuma cikin wadannan shekaru, ta kaddamar da hare-hare da dama.( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China