in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somalia ta zabi shugabannin majalisa gabanin zaben sabon shugaban kasar
2017-01-23 09:46:10 cri
Somaliya ta fara hauwa matakan zaben sabon shugaban kasar bayan da a ranar Lahadi data gabata ta kammala zaben kakakin majalisar dattijan kasar da mataimakansa biyu.

Abdi Hashi Abdullahi, wani masanin harkokin siyasa ne a kasar wanda ya fito daga yankin Somaliland, ya zamanto sabon kakakin majalisar dattijan kasar, wanda aka gudanar mako guda bayan da majalisar wakilan kasar ta zabi nata kakakin.

Abdullahi ya doke abokin karawarsa Mustaf Mohamed Qodah inda ya samu kuri'u 43 shi kuma Qodah ya samu kuri'u 8, kuma nan take Qodah ya amince da shan kaye ya kuma taya abokin takararsa murna.

Dukkannin mutanen biyu sun fito ne daga yankin Somaliland, bisa yarjejeniyar mulkin karba karba da ake gudanarwa a kasar.

Abdullahi, ya taba zama ministan lafiya, da na raya al'adun gargajiya, a lokacin gwamnatin hadin kan kasar tsakanin shekarar 2005 zuwa 2008, zai gudanar da aiki tare da kakakin majalisar wajilan kasar Mohamed Osman Jawari wajen tsara jadawalin zaben shugaban kasar.

A karkashin dokokin zaben kasar Somali na 2016, majalisun dokoki ne suke zabar shugaban kasa, wanda ake bukatar ya samu kashi 2 bisa 3 na adadin kuri'un 'yan majalisar kafin ya yi nasarar zama shugaban kasar.

Sama da 'yan takara 15 zasu fafata a zaben neman shugabancin kasar ciki har da shugaban kasar mai ci Hassan Sheikh Mohamud da firaiministan kasar Abdirashid Omar Sharmarke.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China