in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci Somalia ta bada damar shigar da kayayyakin agaji kasar
2017-03-01 11:14:13 cri
An bukaci Somalia ta cire duk wani tarnaki da ke hana isar kayayyakin jin kai ga al'ummar kasar dake fuskantar matsalar fari, a daidai lokacin da ake tsaka da fuskantar yunwa a kasar dake kahon Afrika.

Mahalarta wani taro da Shugaban kasar Mohammad Abdullahi Mohammad da aka fi sani da farmajo ya kira jiya Talata a birnin Mogadishu, sun bukaci a kawar da sabbin shinge da aka sakawa masu bada agaji a wasu yankuna, dan ba hukumomin bada agaji damar kai dauki ga sama da mutane miliyan shida da matsalar fari ta shafa.

Sanarwar bayan taro da aka fitar, ta ce mahalartan sun amince a dauki matakan da suka dace na kawar da sake aukuwar yunwa a kasar, suna masu gargadi game da barazanar da fari zai haifar ga ci gaban da kasar ta samu cikin shekaru biyar da suka shude.

Sanarwar ta ruwaito mahalarta taron, sun kuma gabatar da kudurin aiwatar da wasu matakai na musamman, da za su magance matsalar fari. Ciki har da fadadawa da inganta harkokin shigarwa da fitar da kayayyakin abinci da samar da tsaro da kara yawan kayayyakin da ake bukata a yankunan dake fama da fari da kuma sake gyara muhimman ababen more rayuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China