in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sudan da Masar sun bayyana kin amincewa da duk wani nau'i na zagi ko cin zarafi
2017-03-22 09:46:33 cri
Sudan da Masar sun bayyana rashin amincewa da duk wani nau'i na zagi ko cin zarafi ga kasashen ko al'ummominsu.

Wata sanarwa ta bayyana cewa, kasashen sun bayyana hake ne yayin wata ganawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Ghandour da takwaransa na Masar Sameh Shukri

Ministocin biyu sun jadadda muhimmancin yin hangen nesa wajen tunkarar abubuwan da masu amfani da kafafen sada zumunta da wasu na yada labarai ke wallafawa, da ka iya yin illa ga manufofin da dangantakar dake tsakanin kasashen da kuma al'ummominsu.

Sun kuma jinjinawa al'adu da tarihin kasashen biyu, suna masu jaddada cewa, kogin Nile shi ne ya hada kasashen da al'ummominsu, wanda kuma ke kara kyautata dangataka dake tsakaninsu tsawon lokaci.

A cewar sanarwar, ministocin kasashen sun amince da gudanar da wani zagaye na taron tuntuba kan harkokin siyasa a birnin Khartoum na Sudan a cikin watan Afrilu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China