A zaben jin ra'ayoyin jama'a da aka yi, ya shafi kudurin doka ta 18 na gyara kundin tsarin mulkin kasar, ciki har da kudurin canja tsarin kasar daga tsarin majalisar dokoki zuwa tsarin shugaba wanda shi ne ya fi jawo hankali sosai. Bisa daftarin gyara kundin tsarin mulikin kasar, za a kafa mukamin mataimakin shugaba guda biyu, kana shugaban kasar zai iya nada mataimakin shugaba da ministocin gwamnatin kasar, kana shugaban kasar zai iya ci gaba da zama shugaban jam'iyyarsa, da a soke mukamin firaministan kasar. Za a kara baiwa shugaban kasar ikon a cikin kundin tsarin mulkin kasar da za a gyara.
Hukumar zaben kasar Turkiya za ta gabatar da sakamakon kidaya kuri'un zaben a hukumance a cikin mako daya. (Zainab)