in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Amurka: lokaci ya yi da a warware batun zirin Koriya ta duk wane hanyoyi ban da amfani da karfin makamai
2017-04-17 10:53:00 cri
Mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka dake kula da harkokin tsaron kasa Herbert McMaster a ranar Lahadin da ta gabata ya ce, kasarsa za ta tabbatar da dukkan wane irin zabe kan batun zirin Koriya. Amma a waje guda kuma ya jaddada cewa, yanzu lokaci ya yi da za a dauki dukkan hanyoyin da suka dace don warware batun cikin lumana ba tare da yin amfani da karfin makamai ba.

Yayin da yake zantawa da kafar yada labarun ABC a wannan rana, Herbert McMaster ya la'anci sabon gwajin harba makamai masu linzami da kasar Koriya ta arewa ta yi, a cewarsa wannan tsokana ce ta lalata zaman karko, ya kuma bayyana cewa, shugaba Donald Trump na kasarsa ya riga ya umurce kwamitin tsaron kasa da ya waiwayi kokarin da ma'aikatar tsaron kasa, ma'aikatar harkokin waje da kuma hukumomin tattara bayyanai na kasar suka yi wajen warware batun zirin Koriya, da nufin samar masa hanyoyin warware batun a lokacin da ya wajabta.

Baya ga haka, Herbert McMaster yana mai cewa, a cikin makwani har ma watanni masu zuwa, bangarori daban daban da batun ya shafa za su samu damar daukar matakai ban da amfani da karfin makamai don hana tabarbarewar halin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China