in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liu Yandong za ta ziyarci kasashen Turkiyya, Jordan, Iran da ma Afirka ta Kudu
2017-04-14 20:28:19 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya sanar a Yau cewa, mataimakiyar firaministan kasar Sin Madam Liu Yan Dong, za ta kai ziyarar aiki a kasashen Turkiyya, Jordan, Iran da ma Afirka da Kudu daga ranar 17 zuwa ranar 27 ga wata, sa'an nan ita da ministan fasahohin wasa da al'adu na kasar Afirka ta Kudu Nathi Mthethwa, za su shugabanci babban taron farko, na tsarin cudanyar al'adu a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu.

Game da ziyarar Liu Yandong a Afirka ta Kudu, Geng Shuang ya nuna cewa, za ta kai ziyarar ce don aiwatar da muhimman ra'ayoyin bai daya, da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kaddamar da tsarin cudanyar al'adu tsakanin kasashen biyu.

Wannan tsari zai kasance irinsa na farko da kasar Sin ta kafa tare da kasashen Afirka, wanda ya shafi hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannonin ilmi, al'adu, kimiyya da fasaha, kiwon lafiya, matasa, mata, kafofin watsa labarai, da masanan ilmi, yawon shakatawa, wasannin motsa jiki, gami da cudanyar jama'a. Wanda zai ba da muhimmiyar ma'ana ga aza harsashin sada zumunta a tsakanin jama'ar kasashen biyu, da inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu daga dukkan fannoni, da kuma habakar cudanyar al'adu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China