Ministan watsa labarai da al'adun Najeriya Lai Mohammed ya ce, gwamnati ta bi dukkan ka'idojin da doka ta tanada wajen gurfanar da alkalan da ake tuhuma da zargin cin hanci da rashawa.
Ministan wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai jiya a Abuja, fadar mulkin kasar, ya shawarci 'yan jarida da su guji jirkita bayanai game da batun gurfanar da alkalan da ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa a kasar.
A cewar ministan, gwamnatin tana yaki da cin hanci da rashawa ne, kuma ba safai ake taba wasu muhimman mutane ba a duk lokacin da ake kokarin kawar da wannan annoba. Lai ya zargi wasu mutane da ke kokarin nuna adawa da matakan gwamnati na yaki da cin hanci a bangaren shari'ar kasar.
Kungiyar lauyoyi ta Najeriya, da kungiyar kwadagon kasar da wasu kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da lamarin.
A kwanakin da suka gabata ne dai 'yan sandan farin kaya suka damke wasu alkalai, bayan da suka samu makuden kudade na kasashe daban-daban a gidajensu. Sai dai a ranar Litinin hukumar tsaron farin kayan kasar(DSS) ta ba da belin alkalan.(Ibrahim)