in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na kokarin tabbatar da budaddiyar gwamnati
2016-10-27 09:41:39 cri

Gwamnatin Najeriya ta ce, a shirye take ta tabbatar da tsarin baiwa 'yan kasuwa na hakika 'yancin da ya dace da nufin tabbatar da budaddiyar gwamnati, da yin adalci, domin baiwa ko wane mutum hakkinsa bisa cancanta.

Darakta janar na hukumar kula da sabunta sha'anin aikin gwamnati Joe Abah, ya shedawa 'yan jaridu a Abuja, babban birnin kasar cewa, manufar wannan shirin ita ce, domin tantance ainihin 'yan kasuwa da suka yi rajista a hukumar dake lura da al'amurran masana'antu ta kasar.

Abah ya ce, a mafi yawan lokuta, akwai masu kamfanoini da dama dake fakewa a inuwar wasu kamfanonin da ba nasu ba.

A cewa Abah, wannan shirin zai taimaka wajen baiwa ma'aikatan gwamnati damar gudanar da tsarin aikinsu ba tare da yin rufa rufa ba, Abah ya ce, wasu da dama daga cikin jami'an gwamnatoci na boye kansu inda suke amfani da sunayen wasu mutane na dabam a kamfanonin da suka mallaka wanda hakan yana kara yaduwar cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa, da yawa daga cikin kwangilolin da gwamnati ke bayarwa, ainihin masu kamfanonin ma'aikatan gwamnati ne ko 'yan majalisu, amma suna yin amfani da wasu sunaye na dabam domin yin rajistar kamfanonin nasu.

Darakta janar din ya shawarci 'yan Najeriya da su fara bayyana irin wadannan ma'aikata masu yin badda kama domin magance rashawa a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China