Dujarric ya bayyana cewa, Sakatare Janar din zai bar birnin NewYork a gobe Juma'a, domin halartar babban taron Tarayyar Afrika karo na 28, da za a yi a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Ya ce sakon Sakatare Janar din ga Tarayyar Afrika, zai mai da hankali ne wajen kulla sabuwar dangantaka cikin mutuntawa da goyon bayan juna, da kuma batutuwan da suka shafi muradun karni masu dorewa.
Ana kuma sa ran Guterres zai gana daya bayan daya da wasu shugabannin kasashen da za su halarci taron, daga bisani kuma ya tattauna da ma'aikatan MDD dake aiki a kasar Habasha. (Fa'iza Mustapha)