in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya nemi goyon bayan bangaren shari'a domin yaki da rashawa a kasar
2016-07-19 10:55:44 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, ya zama wajibi fannin shari'a na kasar ya kasance mai adalci don sauke nauyin dake wuyansa wajen yaki da rashawa a kasar.

Shugaba Buhari ya furta hakan ne a Abuja, babban birnin kasar, a lokacin da ya jagoranci bude taron bita game da rawar da fannin shari'a zai taka wajen yaki da rashawa a kasar.

Kwamitin da shugaban kasar ya kafa game yaki da rashawa ne ya shirya bitar tare da hadin gwiwar cibiyar nazarin al'amurran shari'a ta kasar, da sakariyar kungiyar kasashe renon ingila, da ofishin yaki da miyagun kwayoyi da laifuffua na MDD UNODC.

Shugaban na Najriya ya bukaci bangaren shari'a na kasar da ya kasance a sahun gaba wajen inganta fannin shari'ar domin daukar matakan yaki da rashawa a fadin kasar.

A cewarsa, bangaren shari'a yana da babbar rawa da zai taka wajen yakar rashawa ta hanyar aiwatar da dokokin da suka dace.

Ya ce, fannin shari'ar kasar na da ikon zartas da hukunci cikin gaggawa ga wadanda suka aikata laifuka ba tare da jinkiri ba.

Buhari ya nuna rashin jin dadi game da halayyar wasu lauyoyi wajen amfani da dabarun jan kafa wajen yanke hukunci ga wadanda aka samu da hannu wajen aikata laifukan rashawa, ya ce, wannan lamari yana haifar da tarnaki ga gwamnatinsa a yunkurinta na yaki da cin hanci da rashawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China