Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya da su kara fadada hadin gwiwa, wajen kawo karshen matsalar 'yan gudun hijira dake ci gaba da addabar duniya.
Mr. Wu ya gabatar da wannan kira ne a yayin zaman mahawarar da zauren MDDr ya gudanar game da batun 'yan gudun hijirar a jiya Alhamis. Ya ce, akwai bukatar kasashen duniya su kara azama, wajen aiwatar da yarjejeniyar birnin New York, wadda ta shafi masu gudun hijira da 'yan ci rani.
Kaza lika a cewar sa, ya dace a samar da cikakken iko na aiwatar da ayyukan hukumomin MDD masu ruwa da tsaki a wannan harka, kamar hukumar lura da 'yan gudun hijira ta (UNHCR), baya ga tabbatar da sahihin tsari na kawo karshen matsalar baki dayan ta.
Wakilin na Sin ya ce, a matsayin Sin na kasa mai kujerar din din din a kwamitin tsaron MDD, kuma kasa mai tasowa mafi girma a duniya, za ta ci gaba da ba da dukkanin gudummawa, ta tabbatar da zaman lafiya da ci gaban daukacin sassan duniya.(Saminu)