in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na goyon bayan kokarin da ake na daidaita maganar Syria ta hanyar siyasa
2017-01-20 20:04:04 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Jumma'a cewa, kasar Sin tana goyon bayan duk wata shawara, muddin da ta taimaka wajen warware takaddamar siyasa dake addabar kasar Syria. Kaza lika tana fatan ganin shawarwarin da za a yi tsakanin gwamnatin Syria da bangarori masu adawa da ita, za su kai ga cimma daidaito, da tsagaita bude wuta, tare da samun ci gaba a fannin daidaituwar al'amuran kasar ta hanyar siyasa.

Rahotanni na cewa, bangarorin kasar Syria za su yi muhawara a Astana, fadar mulkin kasar Kzakhstan, a ranar Litinin mai zuwa. Yayin da manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura, ke cewa bangarorin 2, za su maido da shawarwarin da suke yi a birnin Geneva a ranar 8 ga wata mai zuwa.

 Dangane da ci gaban da aka samu, Madam Hua Chunying, ta ce a kullum kasar Sin na da ra'ayin cewa, hanyar siyasa da diflomasiya, ita ce hanyar kadai da za a bi, don kawo karshen rikicin kasar Syria, wanda ya ki ci ya ki cinyewa cikin shekaru 6 da suka wuce. Ban da haka kuma, Madam Hua Chunying ta ce, kasar Sin na goyon bayan MDD, wajen ganin ta taka muhimmiyar rawa, wajen shiga tsakanin bangarorin Syria da ba sa ga maciji da juna. Har wa yau kasar ta Sin na son ganin shawarwarin da za a yi a Astana, sun cimma nasara, tare da kuma share fagen muhawarar da za ta gudana a Geneva yadda ya kamata. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China