in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Rasha ya bukaci a samar da tsaron jiragen karkashin kasa
2017-04-06 10:35:39 cri
A jiya Laraba, firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev, ya sa hannu kan umurnin magance harin ta'addanci da aka kaiwa ayyukan jiragen dake karkashin kasa, kana ya bukaci a kafa rukunin tinkarar ayyukan dake kawo illa ga ayyukan jiragen na karkashin kasa.

Bisa umurnin da aka gabatar a tashar internet ta gwamnatin kasar Rasha, an ce, rukunonin tinkarar ayyukan dake kawo illa ga tsaron jiragen dake karkashin kasa, za su yi sintiri a dukkan lunguna da sako, don tinkarar ayyukan da za su kawo illa ga tsaron jiragen na karkashin kasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China