in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zargi lamarin tashewar bom a tashoshin jirgin kasa dake tafiya a karkashin kasa na Rasha
2017-04-04 12:50:11 cri
A daren jiya Litinin ne kamfanin jiragen kasa masu sufuri ta karkashin kasa na St. Petersburg dake kasar Rasha, ya bayyana wa manema labaru cewa, an riga an maido da ayyukan fusurin jiragen kasan sa a birnin, ban da tashoshin Sennaya Ploschad, da tashar cibiyar Technologichesky, inda aka samu fashewar bom.

Bisa sabuwar kididdigar da kwamitin yaki da ta'addanci na kasar ya fitar, an ce tashin bam da ya auku ya haddasa rasuwar mutane 11, tare kuma da rautatta mutane 45.

Wata sanarwa da kakakin babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya fitar, ta rawaito Mr. Guterres din na la'antar harin na bom, a tashar St. Petersburg. Sanarwar ta ce, babban magatakardar MDDr ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu da alhini ga wadanda suka jikkata, da gwamnati da jama'ar kasar Rasha.

Kaza lika kwamitin sulhun MDD ya gabatar wa kafofin watsa labaru wata sanarwa, inda da babbar murya ya yi tir da harin na bom, tare da kuma kalubalantar masu ruwa da tsaki da su tabbatar da an hukunta masu hannu cikin kitsa wannan ta'asa. Sanarwar ta ce, kwamitin sulhun na Allah wadai da wannan mugun lamari na matsorata, ya kuma jajantawa iyalan mutanen da suka mutu ko suka jikkata, tare da gwamnati da jama'ar kasar Rasha, tare kuma da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka ji raunuka.

A jiya Litinin da misalin karfe 2 da minti 40 na yamma ne wani Bam ya tarwatse a tsakanin tashoshin jiragen kasa na Sennaya Ploschad da cibiyar Technologichesky dake birnin St. Petersburg na kasar ta Rasha. Daga baya kuma, an gano wata na'urar tada bom a tashar dandalin Uprising.

Tuni dai aka shawo kan wannan lamari. Yayin da kuma hukumar gabatar da kararraki ta Rasha ta riga ta bayyana lamari a matsayin aikin ta'addanci.

Kamfanin dillancin labarai na TASS ya bayyana cewa, an riga an tabbatar da mutumin da ake tuhuma da aikata harin wanda da asalin tsakiyar Asiya ne, kuma yana da dangantaka da masu tsattsauran ra'ayi na Syria. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China