Shugaba Xi ya bayyana cewa, ya yi matukar kaduwa da aukuwar wannan lamari mai tada hankali. A cewarsa, kasar Sin na Allah wadai da harin na ta'addanci. Kuma a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin Xi, ya nuna ta'aziyya ga mutane da suka rasu sakamakon lamarin, yana kuma jajantawa wadanda suka jikkata, da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu.
Shugaba Xi ya ce, a wannan mawuyacin hali, jama'ar Sin tana goyon bayan al'ummar Rasha. Kaza lika Sin na matukar adawa da duk wani irin nau'in ta'addanci, tare da fatan karfafa hadin kai tare da kasashen duniya, ciki har da Rasha, da nufin kiyaye zaman lafiya da tsaron duniya, da na shiyya-shiyya. (Bilkisu)