in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar harin da aka kai wa jirgin kasa a Rasha ya kai 14
2017-04-04 17:33:13 cri

Ministar Lafiya ta Rasha Veronika Skvortsova ta ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar harin da aka kai cikin wani jirgin kasan karskashin kasa a garin St. Petersburg na kasar, ya karu daga 11 zuwa 14.

An kai wa jirgin na karkashin kasa hari ne da misalin karfe 11:40 na ranar Jiya Litinin agogon GMT, lokacin da jirgin ke tafiya tsakanin wasu tashoshinsa biyu a birnin St. Petersburg wanda shi ne birni mafi girma na biyu a kasar.

Har yanzu dai ba a san musabbabi ko wanda ya kai harin ba. Amma jami'ai a kasar sun bayyana shi a matsayin harin ta'addanci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China