in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan alkalan kotunan kolin nahiyar Afirka na taro a birnin Khartoum
2017-04-03 12:30:11 cri

Manyan alkalan kotunan koli daga kasashen nahiyar Afirka, na taro irin sa na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar Sudan, domin tattauna hanyoyin inganta sha'anin shari'a a nahiyar.

Da yake jawabi yayin bikin bude taron a jiya Lahadi, shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, ya ce taron wata manuniya ce game da kudurin nahiyar Afirka, na kakkabe tunanin da kafafen yamma ke cusawa a zukatan al'ummar duniya. Daga nan sai ya kalubalanci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC, bisa zargin ta da yayi da siyasantar da ayyukan ta.

A nasa bangare kuwa, shugaban babbar kotun koli ta kasar Sin Zhou Qiang, cewa yayi, taron na wannan lokaci, shi ne irin sa na farko da zai bada damar takarar irin ci gaba da kotunan nahiyar Afirka suka samu.

Cikin wata wasika da ya aike ga taron, Mr. Zhou ya ce matakin hade sassan tsarin shari'ar nahiyar Afirka wuri guda, na da matukar muhimmancin gaske, duba da yadda hakan ka iya bada damar magance yaduwar manyan laifuka da shiyyar ke fama da su, tare da musayar kwarewa a fannin ayyukan shari'a, da kuma fadada damar sanin makamar aiki tsakanin sassan kasashen nahiyar baki daya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China