Mahalarta taron kasa da kasa game da sha'anin sana'o'i na shekarar 2017 (GEC) a Johannesburg sun amince cewar, kudaden tallafi da masu ruwa da tsaka za su samar za su inganta fannin ci gaban sana'o'i a nahiyar Africa.
Ministan ci gaban kananan masana'antu na Afrika ta kudu Lindiwe Zulu, ya fada a jiya Laraba cewa, dukkan masu ruwa da tsaki su kai dauki domin habaka ci gaban sana'o'i.
Zulu ya ce, bangaren sana'o'i suna bukatar a tallafa musu da kayayyakin more rayuwa, da kuma shirye shirye masu inganci. Ya ce, a lokacin da suka tattauna da sauran ministocin kasashen Afrika, sun bayyana cewa, fannin ci gaban kanana da matsakaitan masana'antu SMMEs ba sa samu tagomashi yadda ya kamata a nafiyar Afrika.
Ya ce, ya kamata gwamnatoci su dauki batun ci gaban kananan da matsakaitan masana'antun da muhimmanci. Ya ce, ya kamata a dinga tattaunawa tare da masu kananan da matsakaitan masana'antu gabanin aiwatar da wasu dokoki, da kuma tattaunawa game da batun ci gabansu a ko da yaushe.
Martin Bwalya, babban jami'i a kungiyar raya ci gaban Afrika (NEPAD) ya ce, babbar hanyar da za ta tallafawa ci gaban tattalin arziki da bunkasuwar masana'antu a nahiyar Afrika ita ce inganta kanana da matsakaitan masana'antu.
Bwalya ya bayyana fasaha a matsayin babbar hanyar da za ta taimakawa ci gaban sana'o'i.(Ahmad Fagam)