in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi kan karuwar yunwa a Afirka
2016-12-21 09:32:04 cri

Hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) a talkaice ta yi kashedin cewa, a shekara 2017 da ke shirin kamawa, za a fuskanci matsalar yunwa da tabarbarewar rayuwar al'ummu sakamakon kamfun farin da ya addabi yankin kahon Afirka.

Har ila hukumar ta FAO ta bayyana cewa, ana sa ran yawan karuwar 'yan gudun hijira a yankin gabashin Afirka, za ta kara ta'azza matsala a fannin karancin cimaka, da abinci mai gina jiki da tun farko ake fuskanta, yayin da manoma ke fadi tashin ganin sun magance tasirin matsalar farin da ta abkawa yankin a wannan shekara.

Darektan hukumar mai kula da sashen ayyukan gaggawa da tsugunar da jama'a Dominique Burgeon ya ce, hukumar tana kokarin magance wannan matsala da ta addabi yankin kahon Afirka. Sai dai ya ce, muddin aka taimaka manoma da ke yankin a kan lokaci, babu shakka hakan zai karfafa musu gwiwar zure tasirin farin da halin matsin rayuwar da suka shiga.

Alkaluman da FAO din ta fitar sun bayyana cewa, kimanin mutane miliyan 12 ne a kasashen Habashe, Kenya da Somaliya suke bukatar taimako, yayin da iyalai a yankin ke fama da matsalar abinci da kudin shiga, da karuwar bashi, da karancin alkama da dabbobi da madara da kuma naman da suka samarwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China