in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattijan Najeriya zata binciki kama wasu alkalan kasar
2016-10-20 10:50:52 cri
A jiya Laraba majalisar dattijan Najeriya ta ce za ta yi bincike game da damke 6 daga cikin alkalan kasar wanda jami'an tsaron kasar suka gudanar.

David Umaru shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin shari'a da kare hakkin bil adama na majalisar dattijan, ya tabbatar da hakan a Abuja cewa, dole ne kwamitin zai gayyaci alkalan domin su yi masa karin haske game da batun.

A ranar 8 ga watan nan ne dai, hukumar tsaro ta DSS ta cafke wasu alkalan kasar 6 bisa zarginsu da aikata rashawa.

Majalisar kula da al'amurran shari'a ta kasar NJC ta bayyana cewa, damke alkalan tamkar yin barazana ne ga demokaradiyyar kasar, da yin katsalandan ga fannin shari'a wanda ke da yancin kansa.

NJC ta kara da cewa kama alkalan cin zarafi ne, da rashin mutunta bangaren shari'a. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China