in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Burtaniya ta soma shirye shiryen ficewa daga EU
2017-03-30 14:35:04 cri

A watan Yunin bara ne, kasar Burtaniya ta kada kuri'ar raba gardama game da batun ficewa daga tarrayar Turai wato EU, inda kashi 52 cikin dari na kuri'un suka nuna goyon bayan ficewa daga Turai. Daga nan kuma, kullum gwamnatin Burtaniya tana jaddada cewa, kamata ya yi a girmama ra'ayin jama'arta. Bayan jerin ayyukan da aka yi, a karshe dai a jiya Laraba gwamnatin ta aika da takarda ga shugaban majalisar Turai Donald Tusk don meman ficewa daga kungiyar. A tsakiyar ranar 29 ga wata, shugabar gwamnatin kasar Theresa May ta bayar da sanarwa a majalisar wakilai cewa,

"a 'yan mintoci da suka wuce, a madadina ne wakilin din din din namu dake Turai ya riga ya mika wasika ga shugaban majalisar Turai, don tabbatar da cewa, kasar Burtaniya za ta gudanar da ayar doka ta 50 ta yarjejeniyar Lisbon, kuma a yanzu haka ana gudanar da wasu ayyukan da batun ya shafa. Bisa ra'ayin jama'ar Burtaniya ne, kasar za ta fice daga EU."

Shugaba Theresa ta kuma sake nanata cewa, ko da yake Burtaniya za ta fice daga EU, amma tana fatan EU za ta samu nasara da wadata, kuma za ta iya ci gaba da jagorantar duniya da kuma kare kanta daga barazanar tsaro. Shugabar ta kuma nanata cewa, ko da yake Burtaniya za ta fice daga EU, amma ba za ta bar Turai ba, kasar za ta cigaba da kasancewa babbar kawa da makwabtaciya ta babban yankin Turai.

"A cikin wasikar da na mika wa shugaba Donald Tusk, na riga na tabbatar da cewa, za a kafa dangantakar abokantaka mai zurfi ta musamman, hakan na dacewa da babbar moriyar bangarorin biyu. Ni kuma na tabbatar da cewa, kasar Burtaniya tana so kuma za ta nuna ra'ayi mai yakini don inganta kafuwar irin dangantakar. A yayin shawarwarin ficewa daga EU da za a shafe shekaru biyu ana yinsa, kasar Burtaniya tana fatan EU za ta amince da wannan dangantakar abokantakar."

Theresa May ta kuma jaddada cewa, kafin ficewa daga EU a hukumance, kasarta za ta ci gaba da daukar nauyin dake kanta bisa matsayinta na mambar kungiyar EU, ba za ta gudanar da ikon dokoki kanta ba. Bayan Burtaniya ta fice daga EU a hukumance, kasar za ta janye jiki daga kasuwar bai daya ta kungiyar, tare kuma da neman sa hannu kan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tare da kungiyar. Baya ga haka, gwamnatin ta Burtaniya za ta bayar da takardar bayani game da ficewa daga EU a ranar 30 ga wata, don bayyana matsayinta kan wannan batu.

Za a gudanar da babban zabe a kasashen Faransa da Jamus ba da jimawa ba daya bayan daya, bisa wannan dalili ne manazarta suna ganin cewa, ko da yake Burtaniya ta nemi ficewa daga EU a hukumance, amma duk da haka mai yiwuwa za a yi shawarwari tsakanin bangarorin biyu a bayan watan Nuwamban bana, wato bayan an kafa sabuwar majalisar ministoci a Jamus. Daraktan sashen nazarin batun ficewa daga EU na jami'ar Bermingham City ta Burtaniya, Alex de Ruyter ya bayyana cewa,

"wannan na nuna cewa, watanni kimanin goma kawai da za a yi ta yin shawarwari tsakanin gwamnatin Burtaniya da EU, hakan akwai yiwuwar kasar za ta fice daga EU kafin watan Aflilun shekarar 2019. Wannan ya nuna cewa, Burtaniya za ta fice daga kasuwar bai daya ta EU da kawancen haraji ta kungiyar. Don haka, dole ne gwamnatin Burtaniya ta tabbatar da dokokin da za su kiyaye moriya ga kasar a yayin shawarwarin a tsakaninta da EU."

Yanzu akwai bambancin ra'ayi game da ficewa daga EU a cikin kasar Burtaniya, ko ficewa daga EU zai amfanawa Burtaniya ko a'a, sai dai a zura ido a ga ko yaya zata kaya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China