in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin kare muhalli na MDD ya yi kira da magance haramtaccen cinikin dabbobin Pangolin
2017-02-17 14:14:07 cri
Gabanin bikin ranar dabbobin Pangolin na duniya a gobe Asabar, Shugaban shirin kare muhalli na MDD Ian Somerhalder, ya ce akwai bukatar sabunta matakan yaki da cinikin dabbobin da ake yi ba bisa ka'ida ba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, Somerhalder ya ce cinikin dabbobin pangolin da ake yi ba bisa ka'ida ba a nahiyar Afrika da Asia, saboda bawon jikin suna dauke da magani, zai yi Kankan-kan da wanda ake yiwa giwaye.

Bikin ranar na dabbobin Pangolin, na da nufin wayar da kan jama'a game da matsalar da wadannan dabbobi, da basu da yawa a doron kasa ke fuskanta, wadanda ci gaba da rayuwarsu ya dogara akan kokarin al'ummomin kasashe na kare su daga mafarauta masu sayar da su.

Har ila yau, Somerhalder ya yi gargadin cewa, ci gaba da safararsu da ake ta haramatacciyar hanya a nahiyar Afrika da Asia, zai kai ga karewarsu.

Ya kara da cewa, haramtaccen cinikin dabbobin daji na ci gaba da zama kalubalen ga shirin kare muhalli da wanzar da tsaro da samar da ci gaba a kasashe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China